Isa ga babban shafi
Najeriya

Cutar Lassa na neman zama annoba a Najeriya

Ana kamuwa da Cutar Lassa ne daga bakin Bera
Ana kamuwa da Cutar Lassa ne daga bakin Bera wikimedia
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Gwamnatin Najeriya tace kimanin mutane 40 yanzu suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Lassa Fever da ke naman zama annoba a kasar.

Talla

Yanzu an kara samun jihohin da suka kamu da cutar da suka hada da Filato da Gombe kamar yadda Ministan lafiya Isaac Adewole, ya tabbatarwa manema labarai a jiya juma’a a Abuja.

Yanzu adadin mutane kusan 90 ke dauke da cutar a jihohi da dama ta aka samu bullatarta.

Ana kamuwa da cutar Lassa ne ta hanyar cin abincin da bera ya gurbata ko kuma mu’amala da wadanda ya ke dauke da cutar.

Zazzabin cutar Lassa na yanayi ne da Cutar Ebola mai yin kisa cikin hanzari.

An sanya wa Cutar sunan garin Lassa a cikin Jihar Borno inda aka fara samun bullarta a 1969. Cutar ta bazu a Najeriya zuwa Liberia da Saliyo da Guinea da kuma Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.