Nijar

Kotu ta tantance mutane 15 domin takarar shugabancin Nijar

Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da abokin hamayyarsa na siyasa Hama Amadou
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da abokin hamayyarsa na siyasa Hama Amadou AFP / BOUREIMA HAMA
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 3

Kotun Tsarin Mulki a Jamhuriyar Nijar ta wanke mutane 15 daga cikin 16 da ke nemnan tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi ranar 21 ga wata Fabarairu mai zuwa.

Talla

Daga cikin mutanen da kotun ta tantance d akwai shugaban kasar mai-ci Alhaji Issoufou Mahamadou, da jagoran ‘yan adawa na kasar Alhaji Seini Oumarou, da Hamma Amadou wanda yanzu haka ke tsare a gidan yari bisa zargin sayo jarirai daga Najeriya.

Har ila yau kotun ta wanke daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a cinikin jariran mai suna Abdou Labo, da tsohon shugaban kasar Alhaji Mahaman Ousman.

Kotun dai ta yi watsi da takarar Abdoulkarim Bakasso wanda jam’iyyar PDP Annur ta tsayar a matsayin nata dan takara, saboda a cewar Kotun takardun takararsa ba su cika ba.

Rahoto: An tantance 'Ya takara 15 a zaben Nijar na 2016

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.