Najeriya

Ana kirdadon sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa

Tambarin hukumar zabe a Najeriya
Tambarin hukumar zabe a Najeriya
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 1

A Najeriya yanzu haka hankula sun karkata zuwa ga hukumar zaben kasar domin fitar da sakamakon zaben gwmanan jihar Bayelsa da aka gudanar zagaye na biyu a jiya asabar, yayin da rahotanni ke cewa an samu tashe-tashen hankula a yankuna da dama lokacin zaben.

Talla

Rahotanni sun ce ‘yan bangar siyasa sun kai hare-hare a rumfuna da dama tare da yunkurin sace akwatunan zabe, yayin da wasu majiyoyi ke cewa akwai inda aka samu asarar rayukan jama’a a jiya.

Wasu daga cikin yankunan da aka samu tashe-tashen hankula da kuma kisan jama’a har da yankin Ekeremo, inda aka ce an kashe akalla mutane uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.