Kenya

An bude Jami’ar Garissa ta Kenya

Jami'ar Garissa dake Kenya
Jami'ar Garissa dake Kenya RFI/Sonia Rolley
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

A yau litinin dalibai sun koma daukar darasi a jami’ar Garissa dake kasar Kenya, watanni 9 bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da hallaka mutane 148.

Talla

An bude makarantar ne cikin tsauraran matakan tsaro, inda aka jibge jami’an tsaro cikin shirin ko ta kwana, sai dai dalibai 20 ne kacal suka fara shiga aji domin daukar darasi, a jamai’ar da ke da yawan dalibai 800.

Sai dai kuma watakila hakan nada nasaba da halin firgicin da suka tsinci kansu a ciki watanni 9 baya, da mayakan al-shabab suka kaddamar da wani mummunan hari daya hallaka dalibai 148.

Shamza Abdi wani dalibi ne da ke cewa hakika sun shiga zagayen farko a darasin safe kuma hakika sun dawo. To sai dai da dama daga cikin daliban da ke wajen garin Garissa basu dawo karatun ba, akasarin su ma sun sauya makarantu.

A wancen lokaci da aka kai harin, shugaba Uhuru Kenyata ya bayyana harin a matsayin rashin imani na karshe, ganin yadda maharan suka ware daliban da ba musulmi ba suka hallaka su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.