Isa ga babban shafi
Nijar

Hukumar zaben Najeriya za ta taimakawa zaben Nijar

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da takwaransa na Nijar  Mahamadou Issoufou
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayyana cewa za ta taimakawa takwararta ta Jamhuriyar Nijar, domin ganin an gudanar da kyakkywan zabe a kasar.

Talla

A ranar 21 ga watan Fabrairu ne Nijar za ta gudanar babban zaben shugaban kasa inda ‘yan takara kusan 15 zasu fafata tare da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou.

Najeriya ta bayyana matakin taimakawa Nijar ne bayan Hukumomin zaben kasashen biyu sun gana da juna a Abuja.

Madam Katambe Issoufou, mataimakiyar shugaban hukumar zaben Nijar da ta kawo ziyara Najeriya tace sun nemi taimakon Najeriya ne saboda sun ga an gudanar da karbabben zabe a kasar.

"Muna son mu yi zabe mai kyau a Nijar kamar yadda muka ga an yi zabe mai kyau a Najeriya", a cewar Madam Katambe.

Sannan tace akwai dubarun zabe da dama da suka nema a Najeriya.

Hukumar zaben Nijar dai ta fuskanci kalubalae musamman daga bangaren ‘Yan adawa da suka yi korafin akwai kura-kurai da dama a kundin rijistar masu kada kuri’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.