Isa ga babban shafi
Libya

An yi nasarar kafa gwamnatin hadin kan kasa a Libya

Tutar kasar Libya
Tutar kasar Libya REUTERS/Anis Mili

Wata daya bayan sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna, a yau alhamis an sanar da kafa gwamnatin hadin kan kasa a Libya,abinda masu sharhi ke kallo a wani sabon mataki na mayar da daidaito da zaman lafiya a kasar.  

Talla

Rikici da ya barke a Libya dai ya hallaka daruruwan mutane baya ga tilastawa dubban al’umma tserewa daga kasar, al'amarin dai ya haifar da rudanin siyasa da ya biyo bayan kashe shugaba Moammar Ghadafi a guguwar juyin juya hali na kasashen larabawa

Masu sharhi na ganin cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan zai magance rikicin kasar na tsawon shekaru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.