WFP

Mutane miliyan 14 na fuskantar yunwa a kudancin Afrika

Mutane Miliyan 14 na fuskantar barazanar yunwa a kasashen Malawi da Zimbabwe
Mutane Miliyan 14 na fuskantar barazanar yunwa a kasashen Malawi da Zimbabwe WFP via twitter
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau | Ramatu Garba Baba
Minti 2

Hukumar kula da samar da tallafin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP tace akalla mutane miliyan 14 ke fuskantar barazanar yunwa a kasashen kudancin Afrika sakamakon sauyin yanayin da ya haifar Fari a yankin.

Talla

Hukumar ta yi gargadin cewa Yawan mutanen da zasu fada cikin hali na yunwa na iya karuwa saboda yadda albarkatun gona da aka tanadar ke karewa.

Hukumar WFP tace kusan kashi 10 na mutanen kasar Zimbabwe ma na fuskantar barazanar yunwa saboda daukewar ruwan sama a wasu yankunan kasar.

Hukumar ta ce abin damuwa ne ganin yadda kayayyakin abinci ke tsada a yankin.

Bincike ya nuna cewa shekarar 2015 ta kasance shekara da aka fi samun karancin ruwan sama da albarkatun noma a tsawon shekaru 112 da suka shude a Afrika ta kudu.

Hukumar samar da abincin tace duk da tana fama da matsalar kudi amma tana nazari kan daukar matakan da suka dace domin tunkarar matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.