Isa ga babban shafi
CAF

Najeriya ta doke Nijar ci 4 da 1 a Rwanda

Najeriya ta casa Nijar ci 4-1 a Rwanda
Najeriya ta casa Nijar ci 4-1 a Rwanda CAF
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Najeriya ta casa Nijar ci 4 da 1 a jiya Litinin a gasar cin kofin Afrika ta matasa da ake gudanarwa a Rwanda.

Talla

Kwallaye uku Dan wasan Abia Warriors Chisom Chikatara ya jefa a ragar Nijar bayan Osas Okoro ya fara bude ragar ana dawowa hutun rabin lokaci.

Wasa tsakanin Guinea da Tunisia an tashi ne ci 2 da 2. Yanzu kuma Najeriya ce saman teburin rukuninsu na C da maki 3.

A yau Talata kuma rukunin D zasu kece raini inda makwabtan juna Zambia da Zimbabwe zasu kara a filin wasa na Umuganda a Gisenyi, daga bisani ne kuma Mali zata fafata ne da Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.