An cafke dan Alqa'ida da ya tsere daga kurkukun Mauritania
Wallafawa ranar:
Mahukuntan Mauritnia sun sanar da cafke Cheikh Ould Saleck, dan kungiyar Al Qaeda wanda ya tsere daga gidan yarin makonni uku da suka gabata daidai lokacin da yake jiran a zartas masa da hukuncin kisan da aka yanke masa.
Wata majiyar ‘Yan sanda a kasar ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa an cafke dan Al-qaedan ne lokacin da yake kokarin shiga kasar Guinea Bissau.
Ana zargin Saleck da hannu wajen kai hari akan shugaban Mauritania Mohamed Ould Abdoul Aziz inda a lokacin aka samu asarar jami’an tsaron kasar da kuma wasu daga cikin maharani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu