Burkina Faso

Sojojin Burkina Faso sun kai hari a rumbun makamai

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso AFP/SIA KAMBOU
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Garba Aliyu
Minti 2

Rahotanni daga kasar Burkina Faso na cewa sojin da suka so kifar da gwamnatin kasar a bara sun kai wani kazamin hari a rumbun makamai da ke Ouagadougou babban birnin kasar a yau Juma’a.

Talla

Wata sanarwa da ke fitowa daga rundunar sojin kasar na cewa sojin sun yi katarin murkushe yunkurin harin da aka kai rumbun adana makaman da ke Yimdi mai tazaran kilomita 20 daga Ougadougou.

A cewar sanarwar ba bu hasarar rai, amma kuma an dauki tsauraran matakan tsaro, kuma har an gano mutanen da ke da hannu wajen harin na yau.

Sanarwar na fadin cewa an gano cewa wasu tsirarun sojin da suka yi yunkurin kwace fadar shugaban kasar a bara ne, da har suka yi garkuwa da shugaban kasar na riko suka kai wannan samamen.

Sojin sun ce an gano cewa masu yunkurin na goyon bayan Blaise Campore ne, tsohon shugaban kasar da ya fi dadewa bisa karagar mulki a yammacin Africa, wanda boren da jama’a suka yi masa ya tilasta masa sauka daga mulkin bayan ya yi shekaru 27.

Wasu majiyoyin sun ce yunkurin na yau, sojoji 20 suka kitsa kuma suka aiwatar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.