Ana ci gaba da duba yiyuwar tura dakarun wanzar da zaman lafiya a Burundi
Wallafawa ranar:
Komitin tsaro na MDD da ya ziyarci kasar Burundi, ya gargadi kungiyar tarayyar Afrika bisa son yin amfani da karfin soja a kasar Burundi, dake ci gaba da fadawa a cikin mummunan rikicin siyasar tsawon watanni 8 da suka gabata.
Mambobi 15 da suka hada komitin tsaron na MDD a jiya sun gana da komitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar tarayyar (UA) inda suka tattaunawa kan rikicin sisarar kasar ta Burundi.
Sai dai kungiyar tarayyar Afrika na ci gaba da nuna muhimmancin tura dakarun samar dazaman lafiya a kasar Burudi, a yayin da MDD ta kafe akan neman masalahar rikicin na Burundi ta hanyar tattaunawar siyasa maimakon amfani da karfi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu