Isa ga babban shafi
afrika

MDD ta gargadi cin zarafin mata a Afrika ta Tsakiya

Ana zargin dakarun wanzar da zaman lafiya da cin zarafin 'yan mata a Afrika ta Tsakiya.
Ana zargin dakarun wanzar da zaman lafiya da cin zarafin 'yan mata a Afrika ta Tsakiya. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadi game da sabbin zarge -zargen cin zarafin kananan yara mata da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Turai ke yi a Jamhuriuyar Afrika ta Tsakiya da ke fama da rikice-rikice.

Talla

Majalisar ta ce, ta samu bayanai cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Georgia da Faransa da wata kasa da ba a fadi sunanta ba sun ci zarafin ‘yan matan ta hanyar yi musu fyade.

Tuni dai aka sanar da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da kungiyarr tarayyar Turai kuma sun fara gudanar da bincike akan lamarin.

Babban jami’in kare hakkin dan Adam a majalisar dinkin duniya, Zeid Ra’ad Al Hussain ya ce, zarge-zargen da ake yi wa sojojin na da girma kuma ya kamata a gudanar da bincike sosai akai

To sai dai har yanzu shugabannin kasashen Afrika ba su ce komai ba game da wannan matsalar yayin da kasashen Turai ne kadai suka bayyana damuwarsu kan lamarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.