Benin

An bayyana sunayen yan takara a Jamhuriyar Benin

Thomas Bonin Yayi shugaban Jamhuriyar Benin
Thomas Bonin Yayi shugaban Jamhuriyar Benin © AFP PHOTO / BERTRAND GUAY
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

A Jamhuriyar Benin kotun kolin kasar ta sanar da sunayen yan takara da ta ga sun dace sun tsaya takarar shugabanci kasar na watan fabrairu .Kotun ta bayyana sunayen yan takara 36 da suka cika ka’ida da aka shata ma su na tsayawa takara. 

Talla

Tun bayan da Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya kaffa sabuwar gwamnatin a karkashin jagorancin firaminista Lionel Zinsou wanda kuma jam’iyyar FCBE ta Shugaban kasar ta tsaida a matsayin dan takarar ta mutanen kasar na ci gaba da yi tsokaci a kai.
Masani tsarin tattalin arziki, shugaba Boni Yayi ya dora wa sabon firaministan alhakin tafiyar da ma’aikatar tattalin arzikin kasar,
Wannan dai ne karo na farko da aka taba samu yawan yan takara a wannan karamar kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.