Afrika

Tattaunawa kan batun aikewa da Dakaru zuwa Burundi

Shugaba Mugabe ya na mai yabawa Idris Deby Sabon Shugaban AU
Shugaba Mugabe ya na mai yabawa Idris Deby Sabon Shugaban AU REUTERS/Tiksa Negeri
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

A yau lahadi ne ake kawo karshen taron kungiyar kasashen Afrika na Au dake gudana a birni Addis Ababa na kasar Habasha.Shugabanin kasashen Afrika bayan da suka zabi Idris Deby Shugaban Chadi a matsayin sabon Shugaban kungiyar sun dai bayyana damuwa dangane da batun aikewa da dakaru zuwa kasar Burundi. 

Talla

An nata Shugaban Chadi Idris Derby, sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika, inda ya maye gurbin Robert Mogabe na Zimbabwe.
Shugaban a jawabin sa gaban Shugabanin kasashen Afrika ya ce kasancewar sa a wannan kujera ya na mai fatar gani Shugabanin Afrika sun bashi goyan baya na gani an warware matsalloli da dama dake hadabar Nayihar Afrika.
Ya anbato rikicin dake faruwa a kasashen Sudan ta kudu, Somaliya, Burundi, da yankin Sahel, da kuma rikicin tabkin Chadi, ta hanyar Diplomasiyya kota karfin soji.
Ana sa ran Shugabanin Afrika a yau lahadi za su cimma matsaya dangane da batun aikewa da dakaru zuwa kasar Burundi duk da yake Ban Ki Moon Sakatary Majalisar Dimkin Duniya ya yaba da  shawarar aikewa da dakarun Afrika zuwa Burundi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.