Nijar-Burkina Faso-Australia

Jocelyn Elliot ta dawo Ouagadougou

Jocelyn Elliot yar kasar Australia da shugaban Nijar Mahamadou Issifou a birnin Yamey
Jocelyn Elliot yar kasar Australia da shugaban Nijar Mahamadou Issifou a birnin Yamey

A yau Litinin, Jocelyn Elliot yar kasar Australia da yan Al Qaeda suka saki da kuma ke Nijar ta samu isowa kasar Burkina Fasa.Matar yar shekaru 84 ta sauka tashar sauka dama tashin jiragen sama na birnin Ouagadougou a safiyar litinin daga birnin Yamey cikin jirgin Shugaban kasar Nijar. 

Talla

A ranar 15 ga watan Janairu ne wata kungiyar mai alaka da Al Qaeda ta sace Matar da mijinta Ken Elliot mai shekaru 84.
Kuma bayan sakinta a karshen mako Mahukuntan Australia sun yaba wa kasashen Nijar da Burkina Faso dangane da rawar da suka taka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.