Afrika

Kusan yara miliyan 1 ke fama da karancin abinci a Afrika

Kusan yara miliyan guda ke fama da rashin isasshen abinci mai gina jiki a Afrika.
Kusan yara miliyan guda ke fama da rashin isasshen abinci mai gina jiki a Afrika.

Hukumar UNICEF ta Majalisar dinkin duniya da ke kula da kananan yara ta ce, kusan yara miliyan guda na fama da rashin isasshen abinci mai gina jiki a kasashen gabashi da kudancin Afrika sakamakon fari da matsalar dumamayr yanayi da ake kira el Nino da ta shafi kasashen.

Talla

Rahoton UNICEF ya ce, yara a kasashen na gabashi da kudancin Afrika na fama da matsalar karancin abinci da ruwa mai tsafta yayin da kuma farashin kayyaki ke ci gaba da tsada.

Wannan yanayin ne kuma ke dada jefa iyaye cikin mayuwacin hali na rashin samun isasshen abinci a rana.

Wannan kuma na faruwa ne saboda fari da kuma dumamar yanayin annobar da ake kira El Nino .

Matsalar ta fi shafar yara kanana yayin da rahoton na Unicef ya yi gargadin cewa matsalar za ta ci gaba a shekaru masu zuwa tare da yin kira ga hukumomi a kasashen da su tashi tsaye domin tunkarar matsalar.

Hukumar ta yi kiran tallafin kudi kimanin dala miliyan 87 a Habasha da dala miliyan 26 a Angola da dala miliyan 15 a Somalia da Lesotho da Zimbabwe da matsalar ta shafa.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.