Chadi

Dalibi ya rasa ransa a boren adawa da Fyade a Chadi

Tchadpages.com
Tchadpages.com

Sojojin kasar Chadi sun harbe wani dalibi har lahira tare da jikkata wasu biyar da ke zanga-zangar nuna adawa da fyaden taron dangi da aka yi wa wata budurwa mai suna Zouhoura.

Talla

Jami’in wani asibiti da ke arewacin birnin Faya Largeau ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa da mutuwar dalibin wanda ke makarantar sakandare, kuma shi ne matashi na biyu da aka kashe a zanga-zangar da aka fara mako guda da ya wuce.

Rahotanni sun ce, wasu mutane biyar ne suka sace Zouhoura, sannan suka sanya hotunan tsaraicinta a shafin Internet bayan sun yi lalata da ita, al’amarin da ya tayar da hankulan jama’a matuka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.