EU-TURKIYYA

EU da Turkiyya sun cimma matsaya kan matsalar bakin haure

Shugabanin kasashen tarrayar Turai danaTurkiyya a wajen taron na birnin Brussels
Shugabanin kasashen tarrayar Turai danaTurkiyya a wajen taron na birnin Brussels Reuters/ Yves Herman

Shugabannin kasashen Turai a yau juma’a sun cimma yarjejeniya da kasar Turkiyya domin magance matsalar kwararar bakin daga kasar zuwa yankin na Turai.

Talla

An dai cimma yarjejeniyar ne a birnin Brussels tsakanin shugabannin na Turai da kuma firaministan Turkiyya Ahmed Davutoglu wadanda ke halartar taron kasashen na Turai dangane da wannan matsala.

Tashe-tashen hankula a kasar Syria da Afghanistan shi ya tilastawa miliyoyin mutane tserewa daga kasashen abinda ya haifar da matsalar kwararran bakin haure zuwa nahiyar Turai, al’amarin da aka ce shine mafi muni a tarihi bayan yakin duniya na 2.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.