Mali

An cafke mutane 19 saboda harin Mali

Jami'an tsaro a birnin Bamako na kasar Mali
Jami'an tsaro a birnin Bamako na kasar Mali HABIBOU KOUYATE / AFP

Masu binciken harin da aka kai a birnin Bamako na kasar Mali a ranar litinin da ta gabata, sun ce a halin yanzu sun cafke 19 da ake zargin cewa suna da masaniya a game da wannan hari da aka kai wa shalkwatar rundunar sojin kasashen Turai da ke kasar.

Talla

Masu binciken sun ce, sun samu bayanai masu muhimmanci a cikin wayar tarho ta daya daga cikin ‘yan bindigar da aka kashe, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman daya daga cikin maharan da aka ce an harbe shi da bindiga.

Kasar Mali dai na cikin kasashen Afrika da ke fama da hare-haren mayakan jihadi, abinda ke haddasa hasarar rayukan al’umma musamman fararen hula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI