CAF

CAF ta ci tarar Chadi saboda gasar Afrika

CAF ta ci tarar Chadi saboda ficewa daga gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta 2017.
CAF ta ci tarar Chadi saboda ficewa daga gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta 2017. CAF

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, ta ci tarar kasar Chadi har dala dubu 20 sakamakon janyewar da ta yi daga buga gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta 2017. 

Talla

Kasar Chadi dai ta bayyana cewa rashin kudi ne ya sa ta fice daga gasar, inda ta ce ba za ta iya daukar dawainiyar tafiye-tafiyen jami’anta da 'yan wasanta ba domin buga wannan gasa.

A yau Litinin ne ya kamata Chadi ta ziyarci Tanzania domin fafatawa da tawagarta a filin wasa na Dar El Salam.

Hukmar CAF ta ce, baya ga tarar da aka ci Chadi, har ila yau za ta haramta mata shiga wannan gasar nan gaba.

Yanzu haka, Kasashen Masar da Najeriya da Tanzania ne suka saura a rukuninsu na 7 yayin da Masar ke jan ragamar rukunin da maki hudu sai Najeriya da ke bi mata da maki biyu, sai Tanzania mai maki daya tal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.