Ana Juyayin Shekara Daya Da Kisan Dalibai 148 a Kenya
Wallafawa ranar:
Kasar Kenya na bukin juyayin kisan wulakanci da aka yiwa daliban jami'ar Garissa 148 shekara daya cur yau Asabar.
A cikin jami'ar wasu ‘yan bindiga hudu suka shiga da sunan ‘yan kungiyar Shabab dake Somalia reshen Al-Qaeda suka yi ta kisan dalibai a dakunan barcin su.
Ya kasance kisa mafi muni a kasar tun bayan wanda akayi na mutane 213 da kungiyar Al-Qaeda ta yi sanadin mutuwar su lokacin da aka kai harin bam ofishin jakadancin Amurka dake Nairobi a shekara ta 1998.
A wajen bukin yau Asabar, matasa akalla 100 sun sanya jajayen riguna a jami'ar Garissa suna wakoki
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu