Nijar

An yi gobara a kasuwar Maradi

Harabar wasu shahunan 'Yan kasuwa a Maradi
Harabar wasu shahunan 'Yan kasuwa a Maradi wikimedia

Gobara ta tashi a babbar tashar Maradi da kasuwar Kadro, kuam rahotanni sun ce shaguna sama da 30 suka kone kurmus, sannan mutane sama da goma yanzu haka da gobarar ta taba wadanda suka samu munanan raunuka ke kwance a asibiti.

Talla

‘Yan sanda sun killace inda gobarar ta tashi tare da harba hayaki mai sa kwalla don korar jama'a da ke kokarin satar kayan mutane.

Bayanan farko na cewa man fetur ne da aka à je a wani shago ya haddasa gobarar.

Wannan na zuwa ne bayan wani bangare na kasuwar Wadata a birnin Yamai ya ci wuta jiya Juma’a.

Yanzu haka an fara rejistan sunayen yan kasuwar da wannan bala'i y'a shafa.

Bayanai sun ce da kyar ‘yan kwana kwana suka shawo kan wutar, har sai da aka nemi taimakon motar kashin gobara ta filin jirgin sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.