Nijar

Malaman makaranta na yajin aiki a Maradi

Kofar shiga garin Maradi a Nijar
Kofar shiga garin Maradi a Nijar via-linternaute.com

Daliban makarantun Firamaren gwamnati a Jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar, sun kasance a gida bayan yajin aikin malamansu ‘yan kwantaragi na kwanaki uku sakamakon matsalar rashin albashi tsawon watanni biyu. Wannan matsala dai ta yajin aiki da ta zama ruwan dare na zama karan tsaye ga karatun yara musaman a wannan lokaci na karshen shekara da ake shirin gudanar da jarabawa. Salisu Isa ya aiko da rahoto daga Maradi.