Isa ga babban shafi
Najeriya

"Motoci 36 muka saya akan sama da Naira Miliyan 36 duk guda"

Sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki
Sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 3

Majalisar Dattawan Najeriya ta kare kanta daga zargin sayen motocin kasaita 108 ga mambobinta duk da halin kuncin da al’ummar kasar ke ciki. Majalisar Wakilai kuma tace zata ciyo bashi domin sayen motoci 360 ga mambobinta.

Talla

Shugaban kwamitin ayyuka Sanata Ibrahim Gobir mai wakiltar Sokoto ta Gabas yace Motoci 36 suka saya akan kudi Naira Miliyan 36.5 duk guda sabanin 108 da ake zargin sun saya domin mallakin kowane Sanata.

Senata Gobir wanda kwamitin shi ne ya jagoranci sayen motocin, yace sun saye Motoci 36 ne domin a ba Sanata guda a Jihohin Najeriya 36. A cewar shi ya rage ga Sanatocin da suka fito Jiha guda su sasanta akan wanda zai karbi motar.

Majalisar Wakilai a Tarayya ma tace zata ciyo bashi domin sayo motoci kusan 360 domin rabawa kowane dan Majalisar

Yanzu haka dai ana ci gaba da cece-kuce a Najeriya tare da sukar ‘Yan Majalisun ga matakin sayo motocin.

Sanata Ibrahim Gobir mai wakiltar Sokoto ta Gabas

Kungiyoyi fararen hula a kasar sun ce zasu kaddamar da zanga-zanga domin kalubalantar Matakin sayo wa ‘Yan Majalisun motoci.

Babbar Kungiyar Kwadago ta yi gargadin daukar mataki bayan ta yi kakkausar suka ga matajkin sayen Motocin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.