Najeriya

Najeriya zata kafa kotunan yaki da cin hanci da rashawa

Gwamnatin Najeriya tace ta kusa kammala shirin kafa kotuna na musamman da zasu dinga shari’ar zargin cin hanci da rashawa da kuma satar jama’a ana garkuwa da su dan karbar kudade.Farfesa Itse Sagay, shugaban kwamitin da shugaban kasar ya kafa dan bada shawara kan yadda za’a inganta aikin yaki da cin hanci da rashawa ya bayyana haka.

Tutar Najeriya
Tutar Najeriya
Talla

Farfesa Sagay yace sun kusa kammala aikin su, wanda ake saran shugaba Muhamamdu Buhari zai gabatar ga Majalisa domin amincewa da dokar.
Bangaren shari’a na daga cikin manyan matsalolin da ake zargi da hana ruwa gudu wajen shari’ar wadanda ake zargi  da satar kudaden talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI