Najeriya

Dawo da kudaden da aka sace ne damuwar Buhari

A dawo muna da kudinmu kawai inji Buhari
A dawo muna da kudinmu kawai inji Buhari youtube

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace dawo da kudaden da wasu suka sace suka boye a Birtaniya shi ne damuwar shi, ba neman hakuri daga furucin da David Cameron ya yi akan girman rashawa a Najeriya.

Talla

Shugaban na Najeriya da ke mayar da martani a lokacin da ya ke jawabi kan cin hancin da rashawa a ofishin kungiyar kasashen rainon Ingila, a London, ya ce ya yi matukar kaduwa kuma ya ji kunya game da kalaman Firaministan Birtaniya David Cameron.

Shugaba Buhari ya bukaci gwamnatin Birtaniya ta dawo da kudaden Najeriya da aka boye a kasar.

A jiya Talata ne dai David Cameron ya yi katobara a lokacin da ye ke ganawa da Sarauniyar Ingila, yana mai shaida mata cewa ya gayyaci Najeriya da Afghanistan da cin hanci da rashawa ya yi wa katutu a taron kolin kasar na rashawa da za a soma a ranar Alhamis.

Sai dai Buhari bai ambaci kudaden da ya ke nufi ba. Saidai akwai bincike da gwamnatin Birtaniya ta kaddamar akan Tsohuwar Ministar albarkatun mai da wasu manyan ‘Yan siyasa da suka hada da tsoffin gwamnonin Najeriya.

Kalaman na Cameron ya janyo cece-kuce inda wasu ‘Yan Najeriyar ke ganin ya dace ma Buhari ya kauracewa zaman taron a London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI