Masar

Kotun Masar ta daure mutane 152 saboda zanga zanga

Masu zanga zangar adawa da matakin gwamnatin Masar na mayar da tsibiran maliya ga Saudiya
Masu zanga zangar adawa da matakin gwamnatin Masar na mayar da tsibiran maliya ga Saudiya REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Kotun Masar ta yanke wa wasu mutane 152 hukuncin daurin shekaru biyu zuwa biyar a gidan yari bayan sun yi zanga zangar nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na mayar da tsibiran maliya ga Saudiya.

Talla

Majiyoyoin shari’a sun ce, a halin yanzu, sama da mutane 200 na fuskantar hukukci a  saboda zargin su da karya dokar zanga zanga ta kasar.

Daruruwan jami’an ‘yan sanda aka girke a birnin Alkahira a ranar 25 ga watan jiya domin tarwatsa masu zanga zangar ta nuna adawa da kudirin shugaba Abdel Fatah al Sisi na mika tsibiran Tiran da Sanafir ga kasar ta Saudiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI