Najeriya

Yajin aikin NLC bai samu karbuwa ba a Najeriya

Shugaban Kungiyar Kwadago Ayuba Wabba na zantawa da manema labarai a Abuja
Shugaban Kungiyar Kwadago Ayuba Wabba na zantawa da manema labarai a Abuja REUTERS

Yajin aikin da kungiyoyin kwadagon Najeriya suka bukaci a fara daga yau, bai samu karbuwa sosai ba a mafi yawan sassan kasar.

Talla

Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun bukaci magoya bayansu da su shiga yajin aikin ne bayan da suka gaza cim ma jituwa da gwamnatin kasar domin dawo da tsohon farashin Man fetir bayan gwamnati ta kara kashi 67.

Rahotanni daga jihohin kasar na tabbatar da cewa ma’aikatun gwamnati da kuma bankuna da sauran wurare da ake gudanar da harkoki na yau da kullum sun kasance a bude.

Wakilin RFI a Abuja, Muhammad Kabiru Yusuf ya aiko rahoto.

Yajin aikin NLC bai karbu ba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI