Burundi

Hukumomin Burundi sun nuna damuwa kan wakilin RFI a kasar

Pierre Nkurunziza shugaban kasar Burundi
Pierre Nkurunziza shugaban kasar Burundi REUTERS/Evrard Ngendakumana

Gwamnatin Kasar Burundi ta zargi wakilin Radio France Internationale Esdras Ndikumana da aika da labaran da ba haka suke ba kan tahsin hankali da kisan da ake samu a kasar ta Burundi.

Talla

Ministan tsaron jama’a Janar Alain Guilame Bunyoni ya zargi dan jaridar da kungiyoyin fararen hula da kokarin jefa kasar cikin tahsin hankali saboda irin labaran da suke bayar wa.

Tuni Ndikumana ya bar kasar bayan cin zarafin sa inda yake gudanar da ayyukan sa a kasar waje.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.