Malawi-Amnesty

Amnesty ta zargi 'yan sandan Malawi da kasa kare Zabaya

Kungiyar Amnesty International ta zargi ‘Yan Sandan kasar Malawi da gazawa wajen kare zabaya ganin yadda ake kashe su ake kuma magani da sassan jikin su.

Zabaya na fuskantar barazana karewa ganin yadda ake kashe su don tsafi
Zabaya na fuskantar barazana karewa ganin yadda ake kashe su don tsafi
Talla

Daraktan kungiyar a Yankin Kudancin Afirka, Deprose Muchena yace lallai ‘YanSanda sun kasa gudanar da aikinsu na kare irin wadanan mutane, abinda ya bada damar hallaka su a koda yaushe.

Akalla zabaya 18 aka kasha a cikin watanni 20 da suka gabata, yayin da wasu 5 suka bata, kuma ba a sake jin duriyar su ba.

Matsafa sun yi amanna cewar anfani da sassan jikin zabaya don yin tsafi na kawo arziki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI