Najeria

Tsohon kocin Super Eagles a Najeriya Stephen Keshi ya rasu

Marigayi Stephen Keshi
Marigayi Stephen Keshi

Rahotanni daga Najeriya sun ce tsohon mai horar da ‘yan wasan kwallon kafar kasar kuma kyaftin na Super Eagles Stephen Okechukwu Keshi ya rasu yau yana da shekaru 54

Talla

Emmanuel Ado dake Magana da yawun iyalan sa yace Keshi ya gamu da bugun zuciya daren jiya a dai dai lokacin da yake shirin barin Najeriya.

An dai haifi Keshi a ranar 23 ga watan Janairu na shekarar 1962, kuma shine dan Afirka na biyu da ya lashe kofin nahiyar Afirka a matsayin dan kwallo da kuma mai horar da ‘yan wasa, bayan Mahmoud El-Ghohary.

Keshi ya fara yiwa Najeriya wasa tun yana dan shekaru 20 har zuwa shekarar 1994 da ya jagoranci kasar zuwa lashe kofin Afirka da zuwa gasar cin kofin duniya.

Ya jagoranci Togo da Najeriya zuwa gasar cin kofin duniya, kana kuma ya horar da kasar Mali.

Abokan wasan sa sun yi masa lakabi da ‘Big Boss’
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.