Nijar

Za a yi wa Boko Haram taron dangi a Najeriya

Wasu daga cikin sojojin da ke yaki da Boko Haram
Wasu daga cikin sojojin da ke yaki da Boko Haram naij.com

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar Hassoumi Massaoudou ya ce, dakarun kawance da suka kunshi kasashen Nijar da Najeriya da Chadi da kuma Kamaru za su kaddamar da wani gagarumin farmaki akan mayakan Boko Haram.

Talla

A cewar ministan tsaron na Nijar, za a kaddamar da farmakin ne a yankin arewacin Najeriya da ke iyaka da Nijar wanda ake kallo a matsayin babbar matattarar ‘yan Boko Haram.

Za a gudanar da wannan gagarumin aikin ne a karkashin jagorancin janar Lamidi Adeosun dan Najeriya.

A makon jiya ne, kungiyar ta Boko Haram ta kai wani kazamin hari a sansanin soji da ke garin Bosso na Nijar, inda ta kashe sojoji 26 da suka hada da na Najeriya guda 2 yayi da gwamnatin Nijar ta yi alkawarin daukan fansa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.