Afrika ta Tsakiya

Sabon rikici ya barke a Bangui

Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce akalla mutane uku aka kashe bayan barkewar wani sabon rikici a birnin Bangui inda ake jin karar harbe harbe da muggan makamai.

Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici tun a watan Maris din 2013
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici tun a watan Maris din 2013 MARCO LONGARI / AFP
Talla

Rahotanni sun ce daruruwan mutane suka bar gidajensu bayan barkewar rikicin a unguwar da mafi yawanci musulmi ne a Bangui.

Shaidun gani da ido sun ce an yi amfani da manyan makamai da bindigogin da ke sarrafa kan su.

Sabon rikicin na zuwa ne bayan sace wasu ‘Yan sanda shida a makon jiya. Wannan ya sa ake hasashen ko an yi musayar wuta ne tsakanin ‘Yan sanda da mayakan Seleka.

Ana dai ci gaba da samun tashin hankali bayan rantsar da shugaban kasar Faustin-Archange Touadera a matsayin shugaban kasa.

Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici tun a watan Maris din 2013 bayan mayakan Seleka musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize, Kirista.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI