Bakonmu a Yau

Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan daure Bemba na Congo

Sauti 03:41
Tsohon mataimakin shugaban kasar jamhuriyar Demokradiyar Congo Jean-Pierre Bemba
Tsohon mataimakin shugaban kasar jamhuriyar Demokradiyar Congo Jean-Pierre Bemba REUTERS/JERRY LAMPEN/Pool

Kotun hukunta manyan laifufuka da ke Haque ta bayyana daure tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokiradiyar Congo Jean Pierre Bemba shekaru 18 a gidan yari, saboda samun sa da laifin fyade da kisa da mallakar kungiyar 'yan ina da kisa da kuma cin zarafin Bil Adama. Mai shari’a Sylvia Steiner ta ce, Bemba ya kasa dakilie ayyukan rundunar sojan sa da ya kashe, wadanda suka dinga cin Karensu babu babbaka. A game da wannan batun ne, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami’ar Abuja da ke Najeriya.