Afrika

An samu karuwar safarar miyagun kwayoyi a Afrika

Samfurin irin kwayoyin da ake safararsu daga Afrika zuwa Turai da Amurka
Samfurin irin kwayoyin da ake safararsu daga Afrika zuwa Turai da Amurka REUTERS/Tyrone Siu

Wani rahotan majalisar dinkin duniya ya ce, an samu karuwar safarar haramtattun kwayoyi daga yankin Afrika ta yamma zuwa yankin Asiya da gabas ta tsakiya. 

Talla

Jami’in da ke kula da ofishin yaki da safarar miyagun kwayoyi da kuma aikata laifuka na majalisar da ke kasar Senegal, Pierre Lapague ya ce kwayoyin da aka kwace a Cape Verde da Gambia da Najeriya da kuma Ghana sun kai kashi 78 cikin 100 na hodar ibilis din da aka kwace a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014.

Jami’in ya ce, an samu karuwar safarar hodar ibilis daga Afrika zuwa kasahsen Asiya da kuma gabas ta tsakiya ganin yadda kasuwannin Turai da Amurka suka cika suka batse.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.