Nijar-MDD

Ya dace a taimakawa yan gudun hijira a Nijar

Wani sansani yan gudun hijira a Assaga dake jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar
Wani sansani yan gudun hijira a Assaga dake jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar BOUREIMA HAMA / AFP

A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyi 12 masu zaman kan su na yi kira zuwa kasashen da Majalisar Dinkim Duniya na gani an gaggauta kai dauki zuwa duban yan gudun hijira a yankin kudu maso gabacin kasar,mutanen da rikicin Boko Haram ya tilastawa baro gidajen su.

Talla

A cewar wasu daga cikin kungiyoyin da suka hada da Oxfam, Save The Children sama da yan gudun hijira 50.000 ne ke cikin halin kaka nika yi, karancin abinci, rashi magungunna,wasu daga cikin mutanen na fama da rashin lafiya kadan daga cikin halin da wadannan yan gudun hijira suka samun kan su a cewar wadanan kungiyoyin, harin bayan bayan nan na Boko Haram a garin Bosso ranar 3 ga watan yuni ,al’amarin da ya jeffa rudanni a sanssanonin yan gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.