Najeriya

Amurka ta yi gargadin za a iya kai hari a Lagos

Amurka ta taba cewa za a kai hari a otel din Sheraton na Lagos a watan Mayu
Amurka ta taba cewa za a kai hari a otel din Sheraton na Lagos a watan Mayu RFI/Julie Vandal

Kasar Amurka tace akwai yiyuwar za a kai hare hare a birnin Lagos a kudancin Najeriya a lokacin da ake bukukuwan Sallah tare da yin gargadi ga Amurkawa su yi taka-tsan-tsan da sauraren radiyo domin jin halin da kasa ta ke ciki.

Talla

Ofishin jekadancin Amurka ne ya fitar da sanarwar a yau Talata a yayin da ake shirye shiryen biikin sallah a Najeriya da za a gudanar a gobe Laraba.

Sanarwar tace wasu kungiyoyi masu alaka da ayyukan ta’addanci suna kulle kullen kai hari a otel otel a birnin Lagos yawanci inda baki ‘Yan kasashen waje ke sauka, musamman wadanda ke bakin ruwa.

Sanarwar kuma ba ta ambaci sunan wata kungiya ba da ke shirin kai hare haren, amma ta bukaci Amurkawa su yi taka tsan-tsan tare da kula da muhullin da suka sauka da kuma sauraren kafafen yada labaran Lagos don jin halin da garin ya ke ciki.

Ba dai wannan ne karon farko ba da Amurka ke fitar da gargadin yiyuwar kai hari a Lagos.

Amurka ta taba fitar da irin wannan gargadin a watan Disemban bara da watan Mayun 2014 kan za a kai hari Lagos.

Tun dai soma ayyukan Boko Haram ba a taba kai hari a Lagos ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.