Faransa- Kamaru
Faransa Da Bankin Duniya Za Su Samar da Hasken Wuta a kasar Kamaru
Kasaitaccen Kamfanin Samar da hasken wutan lantarki na kasar Faransa, EDF tare da hadin guiwar Bankin Duniya na shirin hada hannu da Gwamnatin kasar Kamaru domin samar da hasken wutan lantarki da karfin Ruwan kogi akan kudin Turai Euro biliyan daya a Kamaru.
Wallafawa ranar:
Talla
Za'a samar da tashan bada hasken wutan ne a kauyen Natchgal mai nisan kilomita 65 daga birnin Younde.
Tun a bara Gwamnatin kasar ta kulla yarjejeniyar, amma kuma sai cikin watan 10 na wannan shekara ne ake saran za'a fara aikin gadan-gadan.
Ana sa ran a kammala aikin a shekara ta 2021.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu