Fira Ministan Indiya Na Ziyara a Africa ta Kudu
Wallafawa ranar:
Fira Ministan kasar Indiya Narendra Modi ya ziyarci kasar Africa ta kudu a ci gaba da ziyara da ya ke yi a wasu kasashen nahiyar Africa, domin bunkasa harkan cinikayya da kasuwanci da kasashen nahiyar.
Daga kasar Mozambik Narendra Modi ya shiga kasar Africa ta Kudu, a ziyara ta kwanaki biyar da yake yi , inda zai kuma ziyarci kasashen Tanzania da Kenya.
Fira Ministan Indiya tare da mai masaukinsa a Africa ta kudu Jacob Zuma sun sanya hannu cikin yarjeniyoyi masu yawa da suka hada da harkan kimiyyar sadarwa, da yawon shakatawa, da tsaro, da ma'adinai da harkan harhada magunguna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu