Zimbabwe

Ana tuhumar Fasto da yunkurin kifar da gwamnatin Mugabe

Evan Mawarira, Faston da ake tuhuma da tunzura Jama'a a Zimbabwe
Evan Mawarira, Faston da ake tuhuma da tunzura Jama'a a Zimbabwe REUTERS/Philimon Bulawayo

An caji Faston da ke adawa da gwamnati Evan Mawarire da laifin yunkurin kifar da gwamnatin Robart Mugabe tare da yin karan-tsaye ga tsarin tafiyar da gwamnati bayan ya gurfana gaban kotun Harare a yau Laraba.

Talla

Dubban mutane ne dai suka cika kotun makil domin nuna goyon baya ga Faston da ke adawa da shugaba Robert Mugabe.

Faston ya gurfana ne a kotun Harare a yau kan tuhumar da ake masa na tunzira Jama’a.

A jiya ne aka cafke Faston wanda ya kaddamar da yakin adawa da yadda gwamnatin Robart Mugabe ke tafiyar da tattalin arzikin Zimbabwe musamman shafin da ya bude a Twitter da ya samu dimbin magoya baya.

Akwai kuma lauyoyi sama da 50 da suka halarci kotun domin kare faston mai suna Evan Mawarire, Mai shafin Thisflag a Twitter.

Kotun kuma ta caji dan gwagwarmayar da laifin yin karan-tsaye ga tsarin tafiyar da kasa, zargin da kan iya sa a yanke ma shi hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Rahotanni sun ce an bude makarantu da kasuwanni a yau duk da ‘Yan adawa sun bukaci al’ummar Zimbabwe su shiga yajin aiki domin nuna adawa da tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.