Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An kama Pasto saboda bore a Zimbabwe

Pasto Evan Mawarira ya shiga hannun hukumomin Zimbabwe kan zargin sa da tinzira jama'ar kasar don yin bore ga gwamnatin Mugabe
Pasto Evan Mawarira ya shiga hannun hukumomin Zimbabwe kan zargin sa da tinzira jama'ar kasar don yin bore ga gwamnatin Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 1

Hukumomin kasar Zimbabwe sun kama Pastor Evan Mawarire, daya daga cikin masu shirya zanga- zangar adawa da shugaba Robert Mugabe da aka shirya gudanarwa a yau, inda suke tuhumar sa da laifin tinzira jama’a.

Talla

Masu zanga-zangar na bayyana damuwa kan halin tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma mulkin kama-karyar da suke zargin gwamnatin kasar da yi musu.

A makon jiya an gudanar da irin wannan zanga-zangar wadda ta sa aka rufe shaguna da makarantu da kotuna da wasu ma’aikatun gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.