Afrika taTsakiya

‘Yan tawaye sun kashe mutane uku a Afrika ta tsakiya

Mayakan Seleka sun kai hari a  Bambari, na Afrika ta tsakiya
Mayakan Seleka sun kai hari a Bambari, na Afrika ta tsakiya AFP PHOTO / PACOME PABANDJI

Wani sabon fada ya barke a jamhuriyyar Afrika ta tsakiya inda rahotanni suka ce an kashe mutane uku a harin da Mayakan Seleka suka kai a yankin Bambari. Mayakan sun kai harin ne a garin Ngakobo mai nisan kilomita 30 da Bambari.

Talla

‘Yan sanda da suka tabbatar da mutuwar mutane uku sun kuma ce mutane da dama ne suka jikkata bayan sun bude wuta a gidajen mutanen kauyen.

Harin dai ya sa mutane da dama sun tsere daga kauyen zuwa makwabta.

Babu dai cikakken bayani akan dalilin da ya sa mayakan na Seleka suka kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.