Libya

Barazanar fara kai hari akan jiragen ruwa a Libya

Yankin Benghazi na Libya
Yankin Benghazi na Libya REUTERS/Esam Omran al-Fetori

Dakarun da ke biyayya ga gwmanatin Libya da ke birnin Tobruk, sun yi barazana kai hari a kan duk wani jirgin ruwan da ya yi yunkurin shiga kasar domin daukar man fetur.

Talla

Dakarun wadanda ke marawa gwamnatin kasar mai babbar cibiyarta a gabashin kasar, sun ce daga yanzu duk wani jirgin ruwa da ya yi kokarin zuwa yankin domin daukar mai to za su tarwatsa shi nan take.

Janar Abdurrazzaq Al Nadhouri, babban kwamandan askarawan a birnin Tobruk, ya ce ba za a sake daukar mai daga yankin ba sai da amincewarsu.

Mai da shi ne babban azikin da kasar ta Libya ta dogara da shi, inda alkalumma ke cewa yanzu akwai sama da ganga bilyan 48 a kasar, to sai dai sakamakon fadawa yakin basasa a shekara ta 2011, yawan wanda take fitarwa a rana ya yi kasa sosai.

Barazanar ta ‘yan bindiga da ke gabashin kasar ba karamar illa za ta haifarwa gwamnatin kasar da ke birnin Tripoli ba wadda kasashen duniya ke marawa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.