Senegal- Chad

Habre zai biya diyya ga mutanen da ya ci zarafi

Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre
Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre ISSOUF SANOGO / AFP

Wata Kotu a Senegal ta bai wa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre umarnin biyan euro dubu 30 a matsayin diyya ga mutanen da aka ci zarafinsu a lokacin mulkinsa.

Talla

A wannan jumma’ar ce kotun ta bukaci Habre wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a cikin watan Mayun da ya gabata, da ya biya diyyar ga mutanen da aka yi wa fyade ko tsare su ko kuma azabtar da su a zamanin da yake mulkin Chadi a shekara 1982-1990.

Babban alkalin kotun bai Gberdao Gustave, bai ya bayyyana adadin mutane da Habre zai biya wannan diyyar ba.

Amma lauyar da ke kare mutane da aka ci zarafin nasu, Jacqueline Moudeina ta shaida wa ‘yan jaridu cewa, jumullar mutane dubu 4 da 733 ne da suka hada da mutane dubu 1 da 625 da cin zarafin ya shafa kai tsaye, suka shigar da karar Habre a kotun ta musamman.

A yanzu dai , Habre zai biya wadanda aka yi fyade ko kuma lalata da su diyyar CFA miliyan 20 ga duk mutun guda, yayin da kuma zai biya diyyar CFA miliyan 15 ga wadanda aka tsare ko kuma aka kama a matsayin fursunonin yaki.

Su kuwa mutanen da cin zarafin bai shafa kai tsaye ba, zai biya kowannen su diyyar CFA miliyan 10.

Tuni dai kungiyar Amnesty International ta yaba da wannan matakin wanda ta bayyana a matsayin nasara ga mutane da aka keta hakkokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.