RFI Kamaru

Tsawon shekara guda Kamaru na tsare da Wakilin RFI

RFI hausa Correspondent in Cameroon Ahmed Abba
RFI hausa Correspondent in Cameroon Ahmed Abba via facebook profile

Ahmed Abba wakilin Sashen Hausa na RFI a garin Maroua da ke Kamaru, ya share tsawon shekara daya a tsare bayan kama shi a ranar 30 ga watan Yulin 2015 ba tare da an same shi da aikata wani laifi ba.

Talla

Tun cikin watan Fabarairun da ya gabata ne wata kotun soji ta fara yi ma sa shari’a bisa zargin yin hulda da ‘yan ta’adda da kuma kin yin tir da masu aikata laifi.

Hukumar gudanarwa ta kafafen yada labaran Faransa da ke watsa shirye-shirye zuwa kasashen ketare, ta bayyana damuwarta a game da ci gaba da tsare Abba, musamnan lura da yadda aka azabtar da shi tsawon watanni uku a birnin Youande.

A yanzu dai an tsara sake gabatar da shi gaban masu shara’a a ranar uku ga watan gobe.

Ahmed Abba ya share shekara daya a tsare. Ya kamata a kawo karshen tsare shi da ake yi. Bai kamata hukumomin kasar Kamaru su kawar da kai daga wanda ya aikata laifi ba ; Boko Haram ita ce babbar makiyar kasar, amma ba ‘yan jarida ba
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.