Afrika taTsakiya

Afrika ta Tsakiya za ta samu tallafin CFA biliyan 4

Shugaban Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra
Shugaban Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra (Photo : AFP)

Kasashen yankin Tsakiyar Afirka sun sanar da ware kudaden da yawansu ya kai CFA bilyan hudu domin taimaka wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke farfadowa daga matsaloli na yakin basasar da ta yi fama da shi.

Talla

A karashen taron da suka gudanar jiya Lahadi a birnin Malabo na Eqautorial Guinea, kasashen Kamaru da Congo da Gabon da kuma Equatorial Guinea, kowace ta amince ta taimaka da CFA bilyan daya.

Sai dai kasar Chadi wadda ita ma ke fama da nata matsalolin na tattalin arziki ne kadai  ba ta sanar da bayar da nata tallafin ba ga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI