Chad

An rantsar da Idris Deby a karo na biyar

An rantsar da Idriss Déby Itno, a wa'adi na Biyar
An rantsar da Idriss Déby Itno, a wa'adi na Biyar PIUS UTOMI EKPEI / AFP

An rantsar da Idris Deby na Chadi domin yin wa’adin shugabancin kasar karo na biyar a birnin Ndjamena, bikin da aka yi a gaban halartar shugabannin kasashe da dama na Afirka.

Talla

To sai dai an yi wannan biki ne a cikin wani yanayi na zama-zaman dar dar, sakamakon kiran da ‘yan adawa suka yi na gudanar da yajin aiki a yau.

An dai zabi idris Deby ne a cikin watan afrilun da ya gabata, sakamakon wani zabi da ‘yan adawa da ‘yan adawa ke zargin cewa an tafka magudi.

An jibge dimbin jam’ian tsaro a birnin Ndjamena, sakamakon yadda ‘yan adawa suka kudurin aniyar kawo cikas ga wannan bikin na yau, yayin da a jiya lahadi jami’an tsaro suka bindige mutum har lahira a lokacin da ‘yan adawar ke tarzoma.

Jagoran ‘yan adawar Saleh Kebzabo, ya ce suna gudanar da zanga-zangar ta yau ne domin jaddada matsayinsu na rashin amincewa da nasarar a aka ce Deby ya yi a zaben na watan afrilu.

An dai samu halartar shugabannin kasashen da dama na Afirka a wannan biki da aka gudanar a yau, da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya, Issoufou Mahamadou na Nijar, Christian Cabore na Burkina Faso, Muhammad Ould Abdoul Aziz na Mauritania.

Sauran su ne shugaban Sudan, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Equatorial Guinea, Jamhuriyar Benin, Mali da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI