Zambia

Kotu ta baiwa ministoci umarnin ajiye mukaminsu kafin zabe

Kotun Kundin tsarin mulkin kasar Zambia ta baiwa ministocin gwamnatin kasar umurnin sauka daga mukaminsu kafin a gudanar da zaben jibi alhamis.

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu.
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu. AFP PHOTO / CHIBALA ZULU
Talla

Shugaban kasar Edgar Lungu dake fuskantar babban kalubale a zaben ya gyara dokar kasar dan barin ministocin kan kujerar su amma kotun ta sa kafa ta shure.

Su dai ministocin sun fito ne daga Majalisar kasa kuma tuni aka rusa majalisar.

Tuni dai tawagar ‘yan kallo na Kungiyar Tarayyar Turai ta isa a birnin Lusaka domin sa-ido kan yadda za a gudanar da zaben shugabancin kasar na Zambia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI