Zambia

Jam'iyyar adawa na kan gaba wajen samun kuri'u a Zambia

Ana cigaba da tattara sakamakon zabe a Zambia
Ana cigaba da tattara sakamakon zabe a Zambia

Dan takarar shugabancin kasar Zambia karkashin babbar Jam’iyyar adawar kasar Hakainde Hichilema na kan gaba waje samun yawan kuri’un da aka kada a zaben shugabancin kasar yayinda shugaba mai ci Edgar Lungu kebiye masa.

Talla

A jiya ‘yan adawar kasar ta Zambia sun zargi hukumar zaben kasar da kokarin sauya alkalumman zaben shugabancin kasar don dadadawa gwamnati.

Sai dai a nata bangaren hukumar ta ce an samu tsaikon sanar da kashin farko na sakamakon zaben ne saboda yawan al’ummar da suka kada kuri’unsu, sabanin zargin da 'yan adawar kasar suka musu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.