Zambia

Zambia-'Yan adawa na zargin yunkurin magudi a zaben shugaban kasa

Ana cigaba da karbar sakamakon zabe a Zambia
Ana cigaba da karbar sakamakon zabe a Zambia dr

Masu sa ido kan zaben shugaban kasar Zambia, sun bukaci al’ummar kasar, su kwantar da hankulan su sabooda jinkirin da ake samu wajen bayyana sakamakon zaben.

Talla

Sakamakon wucin gadi da hukumar zaben Zambian ta fitar, kawo yanzu ya nuna cewa shugaba mai ci Edgar Lungu na kan gaba da kuri’u 262,149.

Shugaban ‘yan adawar kasar Hichilema ke biye masa da kuri’u 243,794, bayan da aka karbi sakamakon zaben mazabu 29 daga cikin 156 dake kasar.

Sai dai kuma bangaren ‘yan adawa sun ce basu gamsu da sakamakon ba, domin a cewarsu alkalumma da ke hannunsu ya nuna cewa Hichilema ne ke kan gaba, kamar yadda da fari hukumar zaben kasar ta sanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.